Dan wasan Senegal wato Sadio Mané yayi aure da kyakkyawar budurwarsa da suka dade suna soyayya

Dan wasan Senegal wato Sadio Mané yayi aure da kyakkyawar budurwarsa da suka dade suna soyayya

Sadio Mane a hukumance ya fita daga kasuwar soyayya.

Mane, daya daga cikin ‘yan wasan kwallon kafa na Afirka da yayi suna a duniya , ya bai wa magoya bayansa mamaki ta hanyar daura aure da budurwarsa da suka dade suna tareAn gudanar da bikin auren ne a Keur Massar, Dakar, Senegal, inda aka baje kolin sirrin rayuwar winger na Al Nassr. Duk da sirrin da ke tattare da dangantakarsa na tsawon shekaru, labarin auren Mane ya mamaye intanet.Mane ya daura aure da masoyiyarsa Aisha Tamba

Dan wasan tun tana makaranta shi yake daukar nawin karatunta.

Gwarzon dan wasan na Afirka sau biyu ya yi nasarar hana rayuwarsa shiga kafafen yada labarai, kuma bikin ba zato ba tsammani ya kara rura wutar sha’awar jama’a game da aurenAisha ta fito daga gidan talakawa a kasar a Senegal kuma abin sha’awa, ba ta nan a shafukan sada zumunta.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *