Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD ya aza harsashin fara gina Gidaje 250 wanda Gwamnatin Tarayya zata

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD ya aza harsashin fara gina Gidaje 250 wanda Gwamnatin Tarayya zata gina a ƙarƙashin shirin nan na RENEWED HOPE INITIATIVE na Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Aikin ana gudanar da shine a filin dake kallon Jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua dake a cikin garin Katsina..

Gwamna Raɗɗa ya yaba ma Gwamnatin Tarayya akan wannna gagarumin aiki, sai ya bada tabbacin Gwamnatin Jihar Katsina wajen ganin an kammala wannan aiki cikin nasara.

Gwamnan ya kumayi kira ga Ƴan Kwangilar da zasu gudanar da wannan aiki da su tabbata sunyi aiki ingantacce domin cin gajiyar wannan aiki kamar yadda aka tsara.

Sai ya ƙara nanata ƙudirin Gwamnatin Jihar Katsina akan bayar da goyan bayan ta ga Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Tinubu.

Hakanan kuma ya jinjinama Babba da Ƙaramin Ministocin Gidaje da raya birane na Ƙasa akan zaɓar Jihar Katsina domin ƙaddamar da fara wannan gagarumin aiki.

Shima a nashi jawabin, Babban Ministan Gidaje da raya birane, Architect Ahmed Musa Ɗangiwa ya faɗa cewa, za a kammala wannan aiki ne a cikin Watanni Uku kacal kamar yadda Gwamnatin Tarayya tayi yarjejeniya da Ƴan Kwangilar dake gudanar da wannan aiki.

Architect Ahmed Musa Ɗangiwa ya kuma faɗa cewa Matasa sama da dubu shidda ne zasu samu aikinyi a lokacin da ake gudanar da wannan aiki.

Sai yai kira ga Ƴan Kwangilar da su kasance masu kishin Ƙasa wajen yin aiki na gari domin cimma ƙudirin Shugaban Ƙasa na RENEWED HOPE INITIATIVE.

Ya kuma yaba ma Gwamnatin Jihar Katsina akan goyan bayan da take bayar wa domin ganin nasarar wannan aiki.

Waɗan da suka halar ci taron sun haɗa da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruq Lawal, Mai Martaba Sarkin Katsina Dr. Abdulmumini Kabir Usman, Ƙaramin Ministan Gidaje da raya birane, Kwamishinoni, Masu ba Gwamna Shawara, Ƴan Siyasa, Ƴan Kasuwa da dai sau ran su.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *