Tofa Wata Sabuwa Kotu Ta Tasa Keyar Murja Kunya Zuwa Gidan Yari

Tofa Wata Sabuwa Kotu Ta Tasa Keyar Murja Kunya Zuwa Gidan Yari

Kotu Ta Tasa Keyar Murja Kunya Zuwa Gidan Yari

An gurfanar da shahararriyar yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya, a gaban kotun shari’ar addini musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP Kano, bisa zarginta da aikata laifukan kawo batagari cikin dare , aikata badala, tada hatsaniya da kuma razanarwa wanda yin hakan ya saba da sashi na 341, 275 da 227 na kundin SPCL.

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta cafke ta tare da gurfanar da ita a gaban kotun, bayan ta karbi korafe-korafen mazauna unguwar Tishama a karamar hukumar Nasarawa Kano.

Bayan gurfanar da ita a gaban kotun,an karonta mata kunshin zargin, inda ta musanta dukkan tuhumar da ake yi mata.

Lauyan dake kare wadda ake tuhumar Barista Aliyu Umar , Ya roki kotun ta bayar da belin ta, dogaro sashi 35 da 36 na dokokin kasa , da kuma sashi na 168, 172 da 173 na kundin SPCL.

A sanya ta a hannu beli saboda hurimi ne na kotun , sannan idan ta bayar da belin tab a zata gudu ba, ko aikata wani laifi da ya saba da doka’’ Barista Aliyu Umar.

Lauyan gwamnatin jahar Kano da y a wakilci kwamishinan shari’a na jahar Kano, Barista Aminu Umar bai yi suka akan rokon wadda ake tuhumar ba.

Ba mu da suka akan wannan roko domin bayar da beli hurimin kotu ne’’ lauyan Gwamnatin Kano.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed , ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wadda ake zargin a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 22 ga watan fabarairun 2024.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *